Tuesday, September 5, 2017

LABARIN WANI MUTUM MAI TSORAN MUTUWA

LABARIN WANI MAI ƘIN MUTUWA

Akwai wani saurayi mai tsananin ƙin mutuwa. Ba ya son jin ambatonta ko kuma ganin wani abu game da ita.
Saboda tsananin ƙiyayyar da yake yiwa mutuwa, shi yasa ba ya zuwa gaisar da marar lafiya, Ba ya zuwa Jana'iza ballantana gaisuwar mutuwa (Wato Ta'aziyyah).
Tun mutane basu gane halinsa ba, har dai suka fahimci yanayinsa. Abokansa ma sunyi masa nasiha akan haka amma sai ya rika kawo hujjoji marassa tushe domin kare kansa.
Rannan dai sai gashi yayi aure, matarsa ta haifi yarinya mace. Wannan yarinyar ta taso cikin gata da kuma cikakkiyar kulawa daga mahaifinta. Wato yana sonta sosai.
Ana nan, ana nan.. Rannan sai zazzabi ya kama wannan yarinyar. Kafin wani lokaci ta rasu. Mahaifinta (wato wannan saurayin) yayi tsananin bakin ciki sosai.
Yayin da ya fito domin gayyatar mutane wajen jana'izarta akofar gidansa, sai yaga kamar mutane basu damu da mutuwar 'yarsa ba....
Duk inda yaje ya faɗa sai mutane suce "Allah ya jiƙanta" amma babu mai tasowa domin zuwa wajen yi mata sallah.. Kowa yaci gaba da harkokinsa.
Ya wuce cikin gari ya faɗi rasuwar amma da ya dawo unguwarsu sai yaga babu ko mutum guda aƙofar gidansa... Anan ne hankalinsa ya ƙara tashi.
Ya tafi wajen dagacin unguwarsu ya kai ƙarar mutanen unguwa har da Limamin unguwar. Dagaci yasa aka kirawo kamar mutum talatin (30) daga sanannun mutanen Unguwar. Ya tambayesu akan abinda saurayin nan ke zarginsu dashi.
Suka ce masa "ƙwarai kuwa hakane. Gaskiya dama mun daɗe muna jiran wannan ranar. Domin kuwa wannan yaron da kake gani, bai damu da damuwar al'ummah ba. Ba ya gaida marassa lafiya , ba ya zuwa wajen jana'izah ko ta'aziyyah. Shi yasa muma ba zamu sallaci ƴarsa ba".
Daga jin haka sai saurayin nan ya fashe da kuka. Yayi kukan da yafi kukan rashin ƴar tasa. Ya bama jama'a haƙuri, ya tabbatar ma kansa wannan kunkuren.
Su kuma nan take suka yi masa afuwa suka je suka sallaceta suka yi masa ta'aziyyah.
DARASI
********
Wannan labarin na sameshi ne daga bakin wanda abun ya faru a unguwarsu. Kuma na rubutoshi ne domin ya zama izina ga sauran matasa masu irin ra'ayinsa. Waɗanda babu ruwansu da ƴan uwansu Musulmai ko maƙobtansu.
Haƙiƙa kowanne musulmi yana da haƙƙi akan ɗan uwansa Musulmi cewar idan bashi da lafiya yaje ya dubashi. Idan yayi atishawa yayi hamdala shi kuma yayi masa addu'a. Hakanan idan ya rasu yaje yayi masa sallah. Kuma ya rakashi.
Hakanan idan kyakkyawan abu ya sameshi kaje ka tayashi murna. Idan kuma mummunan abu ya same shi kaje kataya shi jaje Allah kasa mudace.

2 comments:

Tafarkin tsira

Fadakarwa

Assalamu Alaikum yan uwana masu girma da daraja inai mufatan Alkairi tare da fatanan kuna cikin ko shin lafiya Ameen, Yan uwa A har kullum m...

Tafarkin tsira